Sinopsis
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.
Episodios
-
Tasirin matakin matatar man Ɗangote ga hada-hadar makamashi a Najeriya
19/04/2025 Duración: 20minShirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani bisa al'ada kan kawo muku amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da ku masu sauraro kuka aiko mana. A yau shirin Tambaya da Amsa zai amsa tambaya wani mai sauraro ne wanda ke neman sani ko kuma ƙarin bayanai game da tasirin matakin matatar man Dangote na daina sayar da ɗanyen mai da Naira, ga tattalin arziƙin ƙasar da kuma yadda hakan zai shafi ɗaiɗaikun jama'a.Don jin amsar wannan tambaya da kuma ƙarin wasu da shirin ya amsa a wannan mako, ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Shirin Sallah na musamman akan muhimmancin azumi ga musulmi
06/04/2025 Duración: 19minKasancewar Azumin na watan Ramadan ya kunshi ladubba da tarin alkhairi a cikinsa, waɗanda suka haɗa ƙara kusanci ga mahalicci ta hanyar gudanar da ɗumbin ibadu da kyautatawa juna da nisantar dukkanin ayyuka ko lamura da suka saɓawa shari’a. Watan na Ramadan wata ne mai matuƙar daraja wanda dukkanin musulmi ke neman falala daga Allah a cikinsa, wakimmu na jihar Bauchi a Najeriya Ibrahim Malam goje ya zanta da Shehin Malami Imam Muhammad Hadi Abubakar, Na'ibin Babban Limamin Masallacin Juma'a na At-Taqwa, da ke garin Bauchi dangane da muhimmancin watan na Ramadana.
-
Bayani akan tsarin ra'ayin riƙau a siyasar Duniya
05/04/2025 Duración: 19minA yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne dangane da ra’ayin riƙau a fagen siyasa wanda jama’a da dama ke neman bayani akansa.
-
Me ye ma'anar kalmomin Kano da Katsina?
15/03/2025 Duración: 18minShirin TAMBAYA DA AMSA da wanan mako tareda Nasiru Sani ya kuma amsa tambaya da wasu suka aiko mana kan muhimmanci Garin Goma na Jamhuriya Dimokradiyar Congo ga 'yantawayen M23. Ku latsa alamar sauti domin jin karin bayani