Al'adun Gargajiya

Yadda sana'ar sassaƙar Turmi ke fuskantar koma baya sabida ci gaban zamani

Informações:

Sinopsis

Shirin "Al'adun mu na Gado" na wannan makon ya yi duba ne akan sana'ar nan ta sassaƙar Turmin, wadda ke a matsayin sana'ar al'adun gargajiya, ko da yake a yanzu samar da na'urori da ke amfanin da Turmin keyi ya mayar da sana'ar baya matuka gaya.    A baya duk macen da za'a kai gidan miji, akan hadata da Turmin babba da ƙarami kana da kuma na ƙarfe wanda za ta rika daka kayan ƙanshi wasu ma hatta Kwalli fari da ake sanyawa jarirai da shi suke dakawa, baya da kuma na da kan sakwara da kuma babba na surfe da daka.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa............