Bakonmu A Yau

Fatima Baba Fugu akan 'yan Najeriya fiye da dubu 24 da suka ɓata

Informações:

Sinopsis

Ƙuniyar Agaji ta Red Cross ta ce yanzu haka akwai mutane sama da dubu 23 da suka ɓata a sassan Najeriya. A bayanin da ta fitar a jiya lahadi, ƙungiyar ta ce 68% na waɗanda suka ɓata dukanninsu mata ne, yayin da jihar Yobe ke matsayin jagora ta fannin yawan waɗanda lamarin ya fi shafa. Fatima Baba Fugu, tana aiki ne da sashen da ke haɗa waɗanda suka ɓata da iyalansu a ƙungiyar ta ICRC daga birnin Maiduguri jihar Borno, ta yi wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal ƙarin bayani a game da waɗannan alkaluma da ƙungiyar ta fitar.