Bakonmu A Yau

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

 • Bakonmu a Yau - Takaddama ta barke tsakanin gwamnatin Bauchi da maaikata kan biyan albashi

  Bakonmu a Yau - Takaddama ta barke tsakanin gwamnatin Bauchi da ma'aikata kan biyan albashi

  04/02/2021 Duración: 04min

  A Najeriya, har yanzu ana kokarin kai ruwa rana tsakanin gwamnatin jihar Bauchi da ma’aikatanta a dangane da biyan albashi da sauran hakkoki. Hakan na faruwa ne a yayin da gwamnatin ta Bauchi ke korafi kan gadar ma’aikatan bogi da ta yi daga wadanda suka gabace, matsalar da take kokarin kawar da ita. Kan haka Ibrahim Malam Goje ya tattauna da Kwamrade Dauda Shu’aibu shugaban kwamitin hadin gwiwar kungiyoyin kwadago a jihar ta Bauchi.

 • Bakonmu a Yau - Tattaunawa Sarkin Fulanin Abeokuta a kan harin da ake kai wa maakiyaya

  Bakonmu a Yau - Tattaunawa Sarkin Fulanin Abeokuta a kan harin da ake kai wa maakiyaya

  03/02/2021 Duración: 03min

  A Najeriya, Fulani makiyaya na cigaba da fuskantar cin zarafi da barazana ga rayukansu da dukiyoyi a yankin kudu maso yammacin Najeriya, bisa zarginsu da aikata muggan laifuka, ciki har da satar mutane don kudin fansa. A baya bayan nan ne, matashin nan mai ikirarin kare hakkin Yarbawa ‘Sunday Igboho’ ya jagoranci kaddamar hare-hare kan makiyayan a jihar Ogun da nufin tilasta musu ficewa daga yankin. Nura Ado Suleiman ya tattauna da AlhajI Muhd Kabir Sarkin Fulanin Abekuta, kuma shugaban kungiyar Miyatti Allah na yankin Kudu maso yammacin Najeriya.

 • Bakonmu a Yau - Tattaunawa da jakadan Najeriya a Nijar Alhaji Rabiu Akawu kan dangantakar kasashen biyu

  Bakonmu a Yau - Tattaunawa da jakadan Najeriya a Nijar Alhaji Rabiu Akawu kan dangantakar kasashen biyu

  02/02/2021 Duración: 03min

  Danganta tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar na cigaba da habaka sakamakon matakai daban daban da gwamnatocin kasashen biyu ke dauka wajen ganin an cimma biyan bukata. Wakilinmu a Jos, Tasiu Zakari ya tattauna da Jakadan Najeriya a Nijar, Alhaji Rabiu Akawu, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

 • Bakonmu a Yau - Tattaunawa da Dr Ahmad Sani Lawal kan juyin mulkin Soji a Myanmar

  Bakonmu a Yau - Tattaunawa da Dr Ahmad Sani Lawal kan juyin mulkin Soji a Myanmar

  01/02/2021 Duración: 03min

  Kasashen Duniya na ci gaba da yin tir kan matakin Sojin Myanmar na hambarar da gwamnatin kasar baya ga tsare shugaban gwamnatin Aung san suu kyi inda kasashen cikin kakkausar murya suka bukaci gaggauta mayar da kasar kan turbar demokradiyya. Sai dai tuni Sojin da suka jagoranci juyin mulkin suka sanar da aniyar shafe wa'adin shekara guda suna jagoranci gabanin mayar da kasar kan turbar Demokradiyya. To ko yaya masana ke kallon juyin mulkin da makomar kasar ta Myanmar, Ahmad Abba ya tattauna da Dr Ahmad Tijjani Lawal masanin siyasar kasa-da-kasa a Najeriya, ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.

 • Bakonmu a Yau - Tattaunawa da Farfesa Balarabe Sani Garko kan dokar sanya kyalen rufe baki da hanci

  Bakonmu a Yau - Tattaunawa da Farfesa Balarabe Sani Garko kan dokar sanya kyalen rufe baki da hanci

  01/02/2021 Duración: 03min

  Kamar yadda watakila kuka ji a cikin labaran duniya, Gwamnatin Najeriya ta sake jaddada matsayin ta na hukunta duk wani mutum da aka samu da laifin kin sanya kyallen dake rufe baki da hanci a bainar jama’a, sakamakon karuwar masu harbuwa da cutar korona da kuma wadanda ke mutuwa. Ya zuwa yanzu adadin mutanen da cutar ta kama a kasar ya zarce 130,000, yayin da kusan 2,000 suka mutu. Dangane da wannan mataki, mun tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, kuma ga abinda yake cewa a kai.

 • Bakonmu a Yau - Tattaunawa da Alzubayr Abubabakr a kan koma baya da aka samu a yaki da rashawa a Najeriya

  Bakonmu a Yau - Tattaunawa da Alzubayr Abubabakr a kan koma baya da aka samu a yaki da rashawa a Najeriya

  28/01/2021 Duración: 03min

  Kungiyar Transparency International a rahoton shekara-shekara da take fitarwa,ta ce Najeriya ta samu koma baya a yakin da take da rashawa Dangane da haka, Abdoulaye Issa ya  tattauna da Barrista Alzubyr Abubakar dake Najeriya, wanda ya bayyana mana irin illar da cin hantsi ke yi wa tattalin arzikin kasashen mu.

 • Bakonmu a Yau - Maaikatan kamfanin COMINAK a Nijar 600 na shirin rasa ayyukansu

  Bakonmu a Yau - Ma'aikatan kamfanin COMINAK a Nijar 600 na shirin rasa ayyukansu

  28/01/2021 Duración: 03min

  A Jamhuriyyar Nijar kimanin ma’aikatan kamfanin hakar Uranium na COMINAK 600 ne ke shirin rasa aikinsu bayan da kamfanin ya sanar da aniyar rufewa a cikin watan Maris mai zuwa sakamakon karancin bukatar ma’adinin na Uranium a kasuwar Duniya. Salisu Isah ya tattauna da Mahamman Laminu shugaban kungiyar ma’aikatan na COMINAK ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.

 • Bakonmu a Yau - Tattaunawa da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa kan nadin sabbin hafsoshin tsaro a Najeriya

  Bakonmu a Yau - Tattaunawa da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa kan nadin sabbin hafsoshin tsaro a Najeriya

  27/01/2021 Duración: 03min

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sabbin manyan hafsoshin sojin kasar, domin maye gurbin wadanda ya nada shekaru 5 da suka gabata. Nadin sabbin hafsoshin na zuwa ne a wani lokaci da matsalolin tsaro suka addabi kasar daga kowane bangare. Dangane da sauyin da aka samu, mun tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya, wanda yayi tookaci akai kamar haka.

 • Bakonmu a Yau - Sakataren kungiyar Miyetti Allah Baba Usman Ngelzerma kan korar makiyaya daga Ondo

  Bakonmu a Yau - Sakataren kungiyar Miyetti Allah Baba Usman Ngelzerma kan korar makiyaya daga Ondo

  26/01/2021 Duración: 03min

  Gwamnonin jihohin yammacin Najeriya tare da na Jigawa da Kebbi da kuma shugabannin Fulani a Yankin da na kasa baki daya da kuma manyan jami’an tsaro sun gudanar da wani taro a Jihar Ondo domin tattauna matsalolin da suka biyo bayan baiwa Fulani umurnin ficewa daga Jihar. Bayan Kammala taron Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da sakataren kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Baba Usman Ngelzerma, kuma ga abinda ya shaida mana.

 • Bakonmu a Yau - Kamaru ta shiga jerin kasashe masu matsalar rashin yiwa yara takardun haihuwa

  Bakonmu a Yau - Kamaru ta shiga jerin kasashe masu matsalar rashin yiwa yara takardun haihuwa

  25/01/2021 Duración: 03min

  Kamaru ta shiga jerin kasashe da akasarin yara basu da takardun shaidar haihuwa, zalika bincike ya nuna cewar tsawon shekaru an daina baiwa jama’a takardun shaidar zama dan kasa. Wannan kalubale ya haifar da fargaba kan makomar yaran da suka rasa shaidar haihuwa, la’akari da cewar da shaidar ake rajistar shiga makarantu. Dangane da wannan batu, Abdoulaye Issa ya tattauna da Barista Hamza Mohammed kuma mai sharhi a kasar ta Kamaru.

 • Bakonmu a Yau - Ambasada Ibrahim Kazaure a kan cikar waadin da aka baiwa Fulani makiyaya su bar dazukan kasashen Yarabawa

  Bakonmu a Yau - Ambasada Ibrahim Kazaure a kan cikar wa'adin da aka baiwa Fulani makiyaya su bar dazukan kasashen Yarabawa

  25/01/2021 Duración: 03min

  Sakamkon cikar wa'adin da aka dibar wa Fulani makiyaya na barin dazukan kasashen kudu maso yammacin Najeriya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ibrahim Kazaure a kan haka.

 • Bakonmu a Yau - Aliyu Dawobe kan haramtawa kasashen duniya amfani da makaman nukiliya

  Bakonmu a Yau - Aliyu Dawobe kan haramtawa kasashen duniya amfani da makaman nukiliya

  22/01/2021 Duración: 03min

  Kungiyar Agaji ta kasa da kasa da ake kira International Red Cross ta bayyana gamsuwa da aiwatar da dokar haramtawa kasashen duniya mallaka, samarwa ko kuma amfani da makaman nukiliya daga yau. Shugaban Kungiyar agajin Peter Maurer ya bayyana matsayinsu cikin wata sanarwa a yau. Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Alhaji Aliyu Dawobe kakakin kungiyar ta Red Cross a Najeriya don sanin tasirin wannan mataki.

 • Bakonmu a Yau - Sama da yan bindiga 500 za su tuba a Kaduna

  Bakonmu a Yau - Sama da 'yan bindiga 500 za su tuba a Kaduna

  21/01/2021 Duración: 03min

  Rahotanni daga jihar Kaduna sun ce sama da ‘yan bindiga 500 ake sa ran za su tuba tare da ajiye makamansu, biyo bayan tattaunawa da fitaccen malamin addinin Musulunci Shiekh Ahmad Gumi a baya bayan nan. A kan haka ne Garba Aliyu Zaria ya tuntube shi, kuma ga yadda tattaunawarsa ta kasance.

 • Bakonmu a Yau - Maryam Muhammad a Amurka kan kalubalen dake gaban sabon shugaba Joe Biden

  Bakonmu a Yau - Maryam Muhammad a Amurka kan kalubalen dake gaban sabon shugaba Joe Biden

  21/01/2021 Duración: 03min

  Shugabannin kasashen duniya na cigaba da aikewa da sakon taya murna ga sabon shugaban Amurka Joe Biden, wanda aka rantsar a matsayin sabon shugaba na 46 a ranar Laraba 20 ga watan nan na Janairu. Mutane a ciki da wajen Amurka na bayyana fatan da suke da ita kan sabuwar gwamnatin. Mun tattauna da Hajiya Maryam Muhammad, malama a kasar ta Amurka, kuma ga tsokacin da tayi akai.

 • Bakonmu a Yau - Fatan yan Afirka ga sabon shugaban Amurka Joe Biden daga masanar nahiyar

  Bakonmu a Yau - Fatan 'yan Afirka ga sabon shugaban Amurka Joe Biden daga masanar nahiyar

  20/01/2021 Duración: 03min

  An rantsar Joe Biden a matsayin sabon shugaban Amurka na 46 domin maye gurbin Donald Trump da ya kawo karshen mulkin sa. Yan Afirka da dama na fatar ganin an samu sauyi dangane da abinda ya shafi dangantaka tsakanin Amurka da nahiyar, sabanin yadda aka gani lokacin shugaba Trump wanda ya kammala wa'adin sa ba tare da ya ziyarci Afirka ba. Dangane da wannan fata da kuma hasashen da ake yiwa sabon shugaban, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Usman Ibrahim na Cibiyar Horar da Yan Majalisu a Afrika, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

 • Bakonmu a Yau - Sunday Bitrus kan kalubalen da sabon shugaban Amurka Joe Biden zai tunkara

  Bakonmu a Yau - Sunday Bitrus kan kalubalen da sabon shugaban Amurka Joe Biden zai tunkara

  20/01/2021 Duración: 04min

  Yau Laraba 20 ga watan Janairu Joe Biden na jam’iyyar Democrat zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka na 46, wanda zai maye gurbin Donald Trump na jam’iyyar Republican, shugaba mai barin gado. Muhimmin batun da a yanzu duniya ta zaku wajen shaidawa shi ne yadda sabon shugaban na Amurka zai tunkari tarin kalubalen dake gabansa na sauya manufofin tsohuwar gwamnatin Donald Trump. Kan haka ne kuma Michael Kuduson ya tattauna da Sunday Bitrus, sakataren kungiyar zumunta, ta ‘yan arewacin Najeriya mazauna Amurka.

 • Bakonmu a Yau - Yan bindiga na ci gaba da cin karensu ba babbaka a sassan Najeriya

  Bakonmu a Yau - 'Yan bindiga na ci gaba da 'cin karensu ba babbaka a sassan Najeriya

  19/01/2021 Duración: 04min

  Kamar yadda kukaji a labaran duniya, Rahotanni daga Gabashin Jihar Sokoto dake Najeriya na nuna cewar yanzu haka Yan bindiga na cigaba da cin karen su babu babbaka wajen kai hare hare suna kashe mutane suna kuma kwashe musu dukiya, tare da yiwa mata fyade. Wannan matsala ta jefa yankin da Jihohin dake makwabtaka da shi da kuma yankunan Jamhuriyar Nijar cikin halin kakanikayi. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sanata Ibrahim Gobir, Dan Majalisar Dattawa dake wakiltar Sokoto ta Gabas, kuma ga yadda zantawar su ta Gudana.

 • Bakonmu a Yau - Tattaunawa da Dr Abdulhakeem Funtua kan rikicin kabilancin da ya halaka mutane 130 cikin kwana 2 a Sudan

  Bakonmu a Yau - Tattaunawa da Dr Abdulhakeem Funtua kan rikicin kabilancin da ya halaka mutane 130 cikin kwana 2 a Sudan

  19/01/2021 Duración: 03min

  Akalla mutane 47 hukumomi suka tabbatar da sun rasa rayukansu a wani rikicin kabilanci can a kudancin Darfur jiya Litinin kwana guda bayan makamancin rikicin a wani yanki daban ya hallaka mutane 80. Jagoran yankin da rikicin ya faru Mohamed Saleh ya ce fadan ya barke tsakanin kabilar Rizeigat da Fallata ne kuma nan ta ke suka fara kashe-kashen daukar fansa tsakaninsu, wanda ke nuna yadda jumullar kusan mutum 130 suka rasa rayukansu a kasa da sa'o'i 30 cikin kasar kwana kalilan bayan ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya. Dangane da wannan, Garba Aliyu Zariya ya tattauna da Dr Abdulhakeem Garba Funtua masanin siyasar kasashe ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.

 • Bakonmu a Yau - Dalilan da suka sa aka gaza shawo kan matsalar tsaro - Kole Shettima

  Bakonmu a Yau - Dalilan da suka sa aka gaza shawo kan matsalar tsaro - Kole Shettima

  18/01/2021 Duración: 03min

  A Nigeria duk da matakan tsaro da hukumomin kasar ke ikirarin suna dauka, ana ci gaba da samun yawaitan satar mutane ana garkuwa da su, a sassan kasar musamman arewaci inda wasu bayanai ke nuna matafiya da masu zaman gida duka basu tsira ba. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Dr Kole Shettima masani kuma mai sharhi dangane da lamurran tsaro a kasar. ko me ya sa aka gaza shawo kan matsalar.

 • Bakonmu a Yau - Najeriya: Matakan da jihar Borno ke dauka don dakile yaduwar Korona

  Bakonmu a Yau - Najeriya: Matakan da jihar Borno ke dauka don dakile yaduwar Korona

  15/01/2021 Duración: 04min

  A Najeriya gwamnatoci kamar takwarorinsu na duniya nata kokarin daukar matakai daban-daban don kawo karshen annobar korona da ta sake bulla a karo na biyu. Jahar Barno dake arewa maso yammacin kasar dake fama da matsalolin tsaro na daga cikin jihohi da suka yaki cutar tun bullarta a karon farko, duk da fargabar da akayi zata iya mummunar illa a jihar saboda tarin ‘yan gudun hijara a jihar. A yayin wata ziyara da Ahmad Abba ya kai birnin Maiduguri, kwamishinan Lafiyar jihar Dakta Salihu Aliyu Kwaya-Bura ya bayyana masa irin matakan da suke dauka.

página 1 de 2