Bakonmu A Yau

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

  • Aminu Kuriga kan kubutar da daliban da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su

    26/03/2024 Duración: 03min

    A ƙarshen makon da ya gabata ne labarin ceto ‘yan makarantar garin Kuriga ta ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna ta Najeriya da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ya karaɗe kafafen yaɗa labarai da shafukan sadarwar intanet.  Sai dai a yayin da hakan ya tabbata a wannan Litinin, ba a samu miƙa waɗannan yara ga iyayensu kamar yadda gwamnatin jihar Kadunar ta alkwarta ba.Dannan alamar saurare don jin tattaunawar sa da Micheal Kuduson.

  • Hon Muktar Ishaq Yakasai kan sukar da wasu ke wa gwamnatin Tinubu

    25/03/2024 Duración: 03min

    Duk da matakai da mahukunta a Najeriya ke cewa sun dauka domin tunkarar manyan matsalolin da kasar ke fama da su, da suka hada da na tsaro da kuma tsadar rayuwa, toh amma mafi yawan al'ummar kasar cewa suke yi a zahirance babu wani tasiri da wadannan matakai ke yi wajen shawo kan wadannan matsaloli. Toh sai dai Hon Muktar Ishaq Yakasai, daya daga cikin magoya bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu, na ganin cewar ya kamata a yi wa shugaban adalci, lura da irin matsalolin da gwamnatinsa ta gada.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.....

  • Mukhtar Bello kan rikicin siyasar Senegal

    22/03/2024 Duración: 03min

    A wannan Juma’a ake kammala yakin neman zaben shugaban Senegal, kasar da rikicin siyasa da ya auku a cikinta a baya-bayan nan ya gaza yin mummunan tasiri a kanta duk kuwa da jan hankalin duniya da lamarin ya yi. Hukumar zaben kasar ta ce kimanin mutane miliyan 7 ne suka yi rajistar kada kuri’a a zaben da ‘yan takara 19 suka raba rana.Masu sharhi da dama sun lura da yadda duk da rikice-rikicen siyasa da suka taso ba a samu wani tashin hankali da ya taka wa shirin zaben birki ba.Kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Dakta Mukhtar Bello, malami a bangaren  kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Farfesa Tukur Abdulkadir kan ziyarar da Blinken a yankin Gabas ta Tsakiya

    21/03/2024 Duración: 03min

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya sake komawa a Yankin Gabas ta Tsakiya a ci gaba da kokarin da kasashen duniya ke yi don samar da tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas. Daga farkon wannan rikici wanda ya barke a ranar 7 ga watan Oktoban bara zuwa yanzu, sau da dama Amurka na cewa tana yunkuri domin samar da tsagaita wuta a wannan yaki da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu 35 da kuma raba sama da milyan biyu da gidajensu. Farfesa Tukur Abdulkadir malami a jami’ar jimi’ar jihar Kaduna, na ganin cewa, da dagaske Amurka ke yi, da tuni an kawo karshen wannan yaki.Ku latsa alamar sauti don jin zantawarsa da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.......

página 2 de 2