Bakonmu A Yau

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

  • Farfesa Kelani kan zargin da NNPCL ta yi wa wasu dillalan mai a Najeriya

    02/05/2024 Duración: 03min

    Kamfanin man NNPCL ya ce yana da wadataccen man da za'a kwashe sama da wata guda ana amfani da shi a cikin gida, yayin da ya zargi wasu gurɓatattun dilallai da jefa jama'ar ƙasar cikin halin ƙunci.  Yanzu haka farashin litar man ya haura naira dubu biyu a wasu sassan Najeriyar, yayin da ake samun dogayen layuka a manyan birane irin su Lagos da Abuja da Kano.Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da farfesa Kelani Muhammed, kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron hirar da suka yi.

  • Nuhu Abayo Toro: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya

    01/05/2024 Duración: 03min

    Yau ce ranar Ma’aikata ta Duniya, kuma bikin na wannan shekara na zuwa ne a cikin mawuyacin hali ga ma’aikatan Najeriya, sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar da kuma kuncin rayuwar da suka samu Kansu.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro, Sakatare Janar na kungiyar kwadago ta kasa ta TUC. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu

  • Dr. Kasim Kurfi: Kan rashin tsayuwar karfin naira

    01/05/2024 Duración: 02min

    Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400. Sai dai a wannan makon Nairar ta sake samun tagomashi inda aka sayar dalar Amurka guda kan kasa da naira dubu 1,300.Ko me ya janyo rashin tsayuwar karfin Nairar, duk da irin matakan da bankin Najeriya ya ɗauka domin ba ta kariya? Tambayar kenan da muka yi Dr Ƙasim Kurfi, masanin tattalin arziƙi a Najeriyar.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar da muka yi da shi

  • Tattaunawa da Nuhu Abbayo Toro na TUC kan ranar ma'aikata a Najeriya

    01/05/2024 Duración: 03min

    Yau ake bikin ranar ma’aikata ta Duniya, wadda a bana ke zuwa a lokacin da ake fuskantar ƙarin matsalolin da a wasu sassa ko kasashe za iya cewa ruɓanyawa suka yi, musamman ma ƙalubalen matsin tattalin arziƙi. A Najeriya ‘Ranar Ma’aikatan ta bana ta zo wa ‘yan Ƙwadagon ƙasar ne cikin yanayin fuskantar tsadar rayuwa, kama daga tsadar kayan abinci, da man fetur har ma da wutar lantarki a baya bayan nan, duk da cewa ba ta samuwa.Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro sakataren kungiyar kwadago ta Najeriya TUC, ga kuma yadda zantawarsu ta gudana game da wannan rana. 

  • Dr Kasim Kurfi kan yadda darajar nairar Najeriya ke kwan-gaba kwan-baya

    01/05/2024 Duración: 02min

    Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400. Sai dai a wannan makon Nairar ta sake samun tagomashi inda aka sayar dalar Amurka guda kan kasa da naira dubu 1,300.Ko me ya janyo rashin tsayuwar karfin Nairar, duk da irin matakan da bankin Najeriya ya ɗauka domin ba ta kariya? Tambayar kenan da muka yi Dr Ƙasim Kurfi, masanin tattalin arziƙi a Najeriyar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

  • Tattaunawa da Bashir Ɗan Malam kan tsadar farashin mai a arewacin Najeriya

    29/04/2024 Duración: 03min

    Harkokin kasuwanci da dama sun durkushe musamman a yankin arewacin Najeriya sakamakon tsadar farashin man fetur, inda ake sayar da lita guda a kan naira 2,000 zuwa 2,500  a kasuwar bayan-fage a jihar Sokoto. Kodayake akwai sassaucin farashin man a yankin kudancin kasar.  Wannan kuwa na zuwa ne bayan watanni 11 da gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur da zummar bai wa kasuwa damar yin halinta. Kan haka Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Alhaji Bashir Dan Malam,shugaban Ƙungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas na Kasa a Najeriya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar

  • Munyi mamakin yadda Amurka ta san bayanan sirrin tsaron mu - Raɗɗa

    26/04/2024 Duración: 05min

    Wasu gwamnonin arewacin Najeriya 10 da ke fuskantar matsalolin tsaro, sun kammala taron da suka je Amurka kan matsalar da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya. Gwamnonin sun ce sun samu bayanan sirrin tsaron jihohinsu a Amurkar fiye da yadda suke samu a Najariya.Ahmad Abba ya tattaunawa da gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Ummaru Radda, wanda ya fara da yi masa bayani kan nasarar taron.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Bashir Dan-Malam kan karancin man fetur a sassan Najeriya

    25/04/2024 Duración: 03min

    Rahotanni daga sassan arewacin Najeriya na nuna cewar an fara samun karancin mai a gidajen mai, abinda ya sa wasu masu man suka kara farashin da suke sayar da kowacce lita. Bashir Ibrahim Idris ya tuntubi daya daga cikin shugabannin dillalan man a Najeriya, Alhaji Bashir Dan-Malam.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Alhaji Shehu Ashaka kan samar da 'yan sandan jihohi a Najeriya

    24/04/2024 Duración: 03min

    Mahawara na ci gaba da zafi a Najeriya, dangane da yunkurin kirkiro ‘yan sandan jihohi domin taimakawa wajen inganta tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a. Yayin da wasu jama’a ciki harda gwamnonin jihohi da tsoffin shugabannin kasa ke cewa lokaci ya yi da za a samar da ‘yan sandan, wasu kuma ciki harda Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar na cewa har yanzu lokaci bai yi ba, saboda gwamnoni na iya amfani da su wajen biyan bukatun kan su. Dangane da wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Shehu Ashaka, daya daga cikin dattawan Najeriya.Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawar su ta gudana.......

  • Arewacin Najeriya aka fi kashe mutane a zangon farko na wannan shekarar - Rahoto

    23/04/2024 Duración: 03min

    Wani bincike da kamfanin Beacon Securities ya yi a Najeriya, ya ce a watanni 3 na farkon wannan shekarar an kashe mutane sama da 2,500, yayin da aka yi garkuwa da wasu sama da dubu 2. Rahotan ya ce kashi 80 na wannan aika aika ana samun sa ne a yankin Arewacin Najeriya. Dangane da haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya.  Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawar su ta gudana......

  • Farfesa Mansur Isa Yelwa kan tsarin almajiranci a Najeriya

    22/04/2024 Duración: 03min

    A karshen makon da ya gabata ne zabtarewar kasa ta hallaka wasu almajirai guda 8 a Jihar Kebbi, matsalar da ta dada  tado da batun kula da almajiran da ke karatun Alkur'ani. Wasu na danganta matsalar da sakacin iyaye wajen rashin kula da 'ya'yan su ko kuma ciyar da su a makarantun allon. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Frafesa Mansur Isa Yelwa, daya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci kuma masanin shari'a a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawarsu.......

  • Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike

    18/04/2024 Duración: 03min

    Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba. Kungiyar tace a cikin shekaru 10 da suka gabata, yankin ya gamu da mummanar ukuba, fiye da sauran sassan Najeriya.Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Dr Murtala Ahmad Rufai na Jami'ar Usman Danfodio, mawallafin 'I am a Bandit' kuma mai bincike a kan matsalar tsaron yankin.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Kuskure ne a yi tunanin ɗagawar darajar naira ba zai ɗore ba - Dakta Kurfi

    17/04/2024 Duración: 03min

    Darajar Naira na cigaba da ɗagawa a Najeriya tare da saukar farashin wasu kayayyakin abinci a wasu kasuwannin ƙasar, abinda ya sa wasu tunanin cewar tasirin saukar Dalar ne ya sanya wasu kayayyakin suka fara sauka. Wane hasashe masana tattalin arziƙi ke yi game da ci gaba da ɗagawar darajar Nairar, tare da zubewar Dala? Tambayar kenan da Abdulkadir Haladu Kiyawa, ya yi wa Dakta Ƙasim Garba Kurfi masanin tattalin arziki a Najeriya yayin tattaunawarsu.

  • Tattaunawa da Sanata Ikira Aliyu Bilbis kan tsaro a jihar Zamfara

    16/04/2024 Duración: 03min

    Hukumomi a Najeriya daga matakin jiha zuwa na kasar baki ɗaya na daukar matakai daban daban wajen samar da zaman lafiya a jihar Zamfara, amma har ya zuwa wannan lokaci ba'a kai ga cimma biyan bukata ba. Ɗan majalisar dattawan da ke wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Ikra Aliyu Bilbis ya ziyarci ofishinmu dake Lagos, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi akan halin da ake ciki.

  • Yadda rayuwa ta kasance bayan da muka faɗa hannun mayakan Boko Haram - Maryama

    15/04/2024 Duración: 03min

    A ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilun nan aka cika shekaru 10 da sace dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok sama da 250 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno. Bayan shafe wannan tsawon lokkaci dai har ya zuwa yau ba a iya gano wasu daga cikinsu ba.Ɗaya daga cikin daliban da suka kuɓuta mai suna Maryama, ta shaidawa Bashir Ibrahim Idris irin abubuwan da suka faru, daga lokacin da aka sace su da kuma lokacin da ta kuɓuta bayan shekaru 3.

  • Kwamred Bello Basi kan shirin gina hanyayoin zamani a Najeriya

    12/04/2024 Duración: 03min

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da kashe naira biliyan 4 kan kowacce kilomita ta hanyar zamani da ake ginawa daga jihar Legas zuwa birnin Kalaba. Gwamnatin ta ce da zarar an kammala aikin za’a samar da shingen karbar kudade guda 50 da za’a rika karbar naira dubu uku kowanne ma’ana zuwa da dawowa mai karamar mota zai rike naira dubu 300, yayin da mai babbar mota da zai rika biyan naira dubu 5 zai rike naira dubu 500 a zuwa da dawowa.An dai yi zargin cewa gwamnatin ta yi amfani da sanayya ne wajen baiwa wani makusancin shugaban kasa wannan kwangila ba tare da bin ka’idojin da suka kamata ba.Kan wannan batu ne, Rukayya Abba Kabara, ta tattauna da Kwamred Bello Basi.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Farfesa Muntaqa Usman kan matakin korar ma'aikata da bankin CBN ya yi

    11/04/2024 Duración: 03min

    Babban Bankin Najeriya CBN na ci gaba da korar wasu daga cikin ma'aikatansa, inda a cikin kwanaki 20 da suka gabata bankin ya sallami ma'aikata 117 akasarinsu manyan ma'aikata. Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Farfesa Muntaqa Usman, masanin tattalin arziki a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawar tasu.......

  • Tattaunawa da Imam Hussien bin Hycinth kan kyautata mu'amala bayan Ramadan

    10/04/2024 Duración: 03min

    Yau al'ummar Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da Sallar Eid el Fitr. Limamin Jami'ar Lagos, Imam Isma'il Musa ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kasance cikin masu hakuri daga halin da suka samu kansu kamar yadda addini ya faɗakar.Bayan kammala hudubar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Imam Hussein bin Hycinth, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

  • Farfesa Mansur Isa kan darussan da ke cikin watan Azumin Ramadan

    09/04/2024 Duración: 03min

    Yau Musulmin duniya ke cika kwanaki 30 da fara azumin watan Ramadana, yayin da ake shirin bukukuwan Sallar Eid el Fitr daga gobe Laraba. Azumin na dauke da darussa da dama da Musulmi ke dauka.Ibrahim Malam Goje ya tambayi Farfesa Mansur Isa Yelwa na Jami'ar Abubakar tafawa Balewa dake jihar Bauchi a arewacin Najeriya, dangane da darussan da ya kamata musulmi ya yi amfani da su.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Baba Sheikh kan matakin yi wa mayakan Boko Haram afuwa da gwamna Zulum ya yi

    08/04/2024 Duración: 03min

    Gwamnatin Jihar Barno da ke Najeriya ta ce akalla mayakan Boko Haram sama da dubu 200 suka rungumi shirin ta na afuwa, inda suka aje makaman su da kuma mika kai domin horar da su da kuma sake musu tunani, kafain mayar da su cikin al'umma. Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ne ya kaddamar da shirin domin bai wa masu bukatar aje makaman su dama. Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Baba Sheikh, mai magana da yawun gwamnan kan wannan batu.Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana.......

página 1 de 2