Sinopsis
Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Episodios
-
Dawowar tsafe-tsafe a tsakanin al'umma
11/03/2025 Duración: 09minShirin Al'adun Mu na Gado na wanan makon tareda Abdullaye Issa ya maida hankali kan dawowa tsafe-tsafe a cikin al'amurran al'umma na yau da kullum.
-
Yadda Gwamnan Adamawa Alhaji Umaru Fintiri ya ƙara yawan Masarautun jihar
25/02/2025 Duración: 10minShirin ''al'adunmu na gado'' tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya leƙa jihar Adamawa ta yankin arewa maso gabashin Najeriya don duba yadda gwamnatin Jihar ta ƙara yawan Masarautu a wannan jiha tun cikin shekarar da ta gabata. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
-
Tasirin naɗin da wasu Masarautu ke yiwa waɗanda ba ƙabilunsu ba
18/02/2025 Duración: 10minShirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan al'adar nan ta naɗin sarauta da wasu masarautun gargajiya ke yi ga ƙabilun da ba su ke da masarautar ba, wanda hakan ya biyo bayan sabbin naɗe-naɗe da ɗaya daga cikin manyan masarautun ƙabilar gwari a arewacin Najeriya ta yi wa wasu manyan shuwagabannin al'ummar fulani a jihar Neja. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun masarautun Hausa da Fulani da ma wasu masarautun a yankin kudanci da kuma arewacin Najeriya ke baiwa ƙabilun da ke zaune a masarautar sarauta ba, abin da shirin Al'adu na wannan mako ya yi nazari akai tare da jin inda hakan ya samo asali da kuma alaƙar da ke tsakanin al'adun ƙabilar gwari da fulani daga masana al'adu da masarautu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
-
Yadda tsamin alaƙar gwamnati da Sarakuna ke raunata Masarautun gargajiya
11/02/2025 Duración: 09minShirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a yau mayar da hankali kan rashin jituwar dake faruwa tsakanin gwamnoni a Najeriya da kuma ɓangaren Sarakunan gargajiya wanda har takai ga wasu jihohin na rushe Masarautu suna kuma kirkirar sababbi. A ‘yan shekarun nan, an sami irin wanann takun saka a jihohi irin Kano da Sokoto da Adamawa da kuma Katsina dukkaninsu a sassan Arewacin Najeriyar, inda masana tarihi da al’adu ke kallon al’amarin a matsayin barazana ga tsarin Sarautar mai dogon tarihi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.