Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Informações:

Sinopsis

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episodios

  • Mabanbantan ra'ayoyin masu saurare kan abubuwa da dama

    21/06/2024 Duración: 10min

    RFI Hausa na bai wa masu saurare damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya a kowacce ranar Juma'a. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan matakin IPOB na shiga tattaunawa da Najeriya

    20/06/2024 Duración: 10min

    Jagoran IPOB da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu, ya ce a shirye yake ya shiga tattaunawa da gwamnati domin kawo ƙarshen kai-da-kawon da ake yi da shi a gaban kotu. Kanu, wanda mahukuntan ƙasar Kenya suka kama tare da miƙa wa Najeriya shi tun a 2021, yanzu haka yana fuskantar tuhume-tuhume ciki har da na ta’addanci da kuma cin amanar ƙasar.Shin ko tattaunawa ita ce mafita don warware wannan al’amari?Ko wataƙila sakin Nnamdi Kanu zai iya taimakawa domin samar da zaman lafiya musamman a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Ayeeshat Jibrin Ahmed

  • Ra'ayoyi kan rikici tsakanin Nijar da Benin

    19/06/2024 Duración: 10min

    Rikici tsakanin Nijar da Jamhuriyar Benin, ga alama zai iya ɗaukar dogon lokaci kafin a iya warware shi, saboda ko bayan rufe iyaka, Nijar ta rufe bututun da ke isar da ɗanyan mai zuwa Cotonou. Wani abu da ya ƙara zafafa wannan rikici shi ne, kama wakilan da Nijar ta tura don sanya ido game da yadda ake fitar da man, inda aka yanke musu hukuncin daurin talata na watanni 18 a kasar ta Benin.Anya akwai alamun ƙasashen biyu za su sulhunta wannan rikici da ke tsakaninsu?Wane tasiri ku ke ganin cewa wannan rikici wajen hana cuɗanya ta tattalin arziki a tsakanin wadannan ƙasashe?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin

  • Ra'ayoyi kan samar wa da Afrika alluran rigakafin cututtuka

    18/06/2024 Duración: 10min

    Gabanin taron da za a gudanar ranar Alhamis a birnin Paris don taimaka wa Afirka dangane da yadda za ta samar wa kanta da alluran rigakafin kariya daga wasu cututuka a wadace, tuni aka samu alƙawurran sama da Euro biliyan ɗaya daga ƙasashe da da kuma ƙungiyoyi daban daban a cewar fadar gwamnatin Faransa. Wadannan kuɗade za a yi amfani da su ne don tabbatar da cewa kamfanonin sarrafa magunguna sun samar da alluran rigakafin cututuka kamar Korona, Cholera da kuma zazzaɓin cizon sauro a cikin nahiyar.Shin me za ku ce a game da wannan tallafi na ƙasashen duniya zuwa ga nahiryar Afirka?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin

  • Ra'ayoyin Masu Saurare kan farashin raguna

    13/06/2024 Duración: 09min

    Yayin da ya rage kwanaki kaɗan a gudanar da Sallar Idil-kabir wato sallar layya, yanzu haha hankulan mafi yawan jama’a sun karkata zuwa ga batun sayen ragunan layya.Yaya farashin raguna da kuma sauran dabbobin da ake layya da su a kasashenku?Shin ko yanayin da ku ke ciki a yau, zai ba ku damar yanka dabbar layya a wannan shekara? Wannan shi ne abin da shirin ya tattauna a kai.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

  • Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun yi watsi da sabon harajin da CBN ya bullo da shi

    09/05/2024 Duración: 10min

    Ƙungiyar Ƙwadago da sauran kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi fatali da matakin gwamnati na baiwa bankuna umarnin fara cirar harajin kashi 0.5 wato rabin ɗaya kenan cikin 100, kan duk hada-hadar aika kudaden da ‘yan kasar ke yi ta intanet. A cewar gwamnatin za a rika amfani da sabon harajin don samar da tsaro daga barazanar masu yi wa mutane kutsen satar kuɗaɗe da sauran muhimman bayanai ta shafukan intanet.Sai dai ƙungiyoyin sun ce sabon harajin zai sake jefa ‘yan Najeriya musamman matsakaita da masu ƙaramin ƙarfi ne cikin ƙarin ƙunci, bayan matsin da suke ciki.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Kan gudun mowar Japan ga yankin Sahel wajen yaki da ta'addanci

    02/05/2024 Duración: 09min

    Bayan kammala ziyarar kwanaki biyu da ministar harkokin wajen ƙasar ta kai a Najeriya, gwamnatin Japan ta ce za ta bayar da gudun mowa domin yaƙi da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel. A tarihi dai ba kasafai Japan ke shiga batutuwan da suka shafi yaƙi da ta’addanci ba a duniya, abin da ya sa wasu ke ganin cewa duk wani tallafi da zai fito daga ƙasar zai kasance mai alfanu wajen yaki da wannan matsala.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Kan matakin rufe wasu kafafen yada labarai da gwamnatin sojin Burkina Faso ta yi

    30/04/2024 Duración: 10min

    Ƙasashen duniya da kuma ƙungiyoyi kaƙƙin aikin jarida da kuma ‘yancin bayyan ra’ayi, sun yi tir a game da matakin rufe wasu kafafen yaɗa labarai da gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta dauka. Baya ga kafafen yada labaran Faransa ciki har da RFI da kuma France24, matakin rufe kafafen yaɗa labaran ya shafi na Amurka, Birtaniya Faransa da dai sauransu domin kawai wallafa rahoton kungiyar HRW da ke zargin dakarun gwamnati da yi wa fararen hula kisan gilla.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkeen shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama

    26/04/2024 Duración: 09min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a ya bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu ne game da batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro, zaman-takewa da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

  • An fara samun karancin man fetur a sassan Najeriya

    25/04/2024 Duración: 10min

    Rahotanni daga sassan arewacin Najeriya na nuna cewar an fara samun karancin man fetur a gidajen sayar da man, abinda ya sa wasu masu man kara farashin da suke sayar da kowacce lita. Ko menene ya haddasa matsalar karancin man fetur din a sassan kasar?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Kan halin rashin tsaron da arewa maso yammacin Najeriya ke ciki

    18/04/2024 Duración: 10min

    Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa da ake kira Global Rights ta bayyana cewa yankin arewa maso yammacin Najeriya shi ne mafi fuskantar ayyukan ta’addanci masu alaka da kashe-kashe ko garkuwa da mutane idan an kwatanta da yankin kudancin kasar. Rahoton da ya bayyana halin da ake ciki a yankin na arewa maso yammacin Najeriya da wani lamari mai tayar da hankali wanda kuma al’umma ba za su lamunci ci gaba da wanzuwarsa ba, ya ce wajibi ne mahukuntan kasar su lalubo hanyoyin warware matsalolin wannan yanki.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • An cika shekara guda da fara yakin kasar Sudan

    16/04/2024 Duración: 10min

    A farkon wannan makojn ne yakin da ake gwabzawa a Sudan tsakanin sojojin kasar karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun RSF da ke karkashin Mohamed Hamdan Dagalo ke cika shekara guda. Rikicin da aka faro a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2023, ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama da kuma raba miliyoyi da muhallansu, wanda a yanzu MDD ta ce akwai barazanar barkewar yunwa a kasar.Bangarori da dama ne dai suka yi yunkurin warware wannan rikici amma abin yaci tura.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.

  • Kan cika shekaru 10 da sace daliban Chibok da Boko Haram ta yi

    15/04/2024 Duración: 09min

    Yayin da aka cika shekaru 10 da sace dalibai a makarantar sakandiren 'yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, har yanzu akwai matan kusan 100 da ke tsare a hannun mayakan Boko Haram da suka yi garkuwa da su. Gwamnatin kasar dai na ci gaba da ikirarin cewa, tana iya bakin kokarinta wajen ganin an sako sauran 'yan matan da ke hannun mayakan.Abin tambayar ita ce, wannen hali iyayen yara da ke hannun mayakan ke ciki?Yaya makomar ilimi take a Najeriya, tun daga lokacin da Boko Haram suka kafa tarihin sace dalibai kawo yanzu?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama

    12/04/2024 Duración: 09min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a ya bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu ne game da batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro, zaman-takewa da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama

    05/04/2024 Duración: 10min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a ya bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu ne game da batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro, zaman-takewa da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

  • Gamnonin Najeriya sun ciyo bashin kusan dala biliyan biyu

    03/04/2024 Duración: 10min

    Kasa da shekara guda bayan rantsar da sabbin gwamnonin Najeriya, 13 daga cikin su, sun ciyo bashin da yawan sa ya kai dala biliyan 2 daga kasashen waje ko kuma cibiyoyin bada lamuni daban-daban. Cin bashi a tsakanin gwamnatocin Najeriya ba sabon abu bane sai dai kuma abinda ‘yan kasar ke fargaba shine idan har an ciyo wannan adadin bashi a kasa da shekara guda, nawa za’a ciwo cikin shekaru 4.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa.

  • Sabon shugaban Senegal ya karbi rantsuwar kama aiki

    02/04/2024 Duración: 10min

    A ranar Talata ne aka rantsar da sabon shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, wanda ya lashe zaben kasar a makon da ya gabata da kaso sama da 54 cikin 100 na yawan kuri’u sama da miliyan 7 da aka kada. Faye shine shugaba mafi kankantar shekaru a Afrika, kuma ya lashe zaben ne a wani yanayi da kasar ke cikin chukumurdar siyasa.Matashin ya zama shugaban kasa ne kasa da makonni biyu bayan fitowar sa daga gidan yari.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Yadda Kiristoci suka gudabnar da bikin Easter a fadin duniya

    01/04/2024 Duración: 09min

    Kiristoci a fadin duniya su na gudanar da bukukuwan Easter, ranar mai mahimanci da ke zagayowa duk shekara don tunawa da sadaukarwar da Isa Almasihu ya yi domin duniya, wadda a cikin sakon Paparoma Francis yai kira ga duniya bisa kiyaye afkuwar yaki kowanne iri. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Sakamkon zaben kasar Senegal na ci gaba da daukar hankali

    27/03/2024 Duración: 09min

    Dan takarar adawa Bassirou Diomoye Faye wanda ke tsare a gidan yari har zuwa jajibirin zabe, zai kasance shugaban kasar Senegal kamar yadda alkaluman zaben da aka yi ranar lahadin da ta gabata ke nunawa. Shin wanne irin gagarumin sauyi aka samu a fagen siyasar kasar Senegal inda dan adawa ya kayar da dan takarar jam’iyyar da ta share shekaru 12 kan karagar mulki?Wanne irin mataki al'ummar Senegal suka dauka na samar da wannan sauyi cikin kankanin lokaci, musamman lura da irin rikice-rikicen da kasar ta yi fama da su a baya, amma duk da haka aka yi wannan zabe a cikin kwanciyar hankali?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Karin kudin aikin Hajjin bana a Najeriya ya shafi maniyyata da dama

    26/03/2024 Duración: 10min

    Hukumar alhazai a Najeriya, ta sanar da karin kusan Naira milyan biyu a kan kujerar aikin hajjin bana ga maniyatan da suka riga suka zuba kudadensu. Wannan dai mataki ne da ya yi matukar bai wa jama’a mamaki, tare da kara haifar da fargar cewa dubban maniyata ba za su iya sauke faralin na shekarar bana ba.Abin tambayar shine, wane tasiri wannan mataki zai yi a kan maniyatan Najeriya na shekarar bana?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

página 1 de 2