Sinopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodios
-
Ra'ayoyin Masu Saurare kan batutuwa daban daban
06/09/2024 Duración: 10minRFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinku kan batutuwa daban daban da ke ci musu tuwo a ƙwarya a kowacce ranar Juma'a. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan tasirin taron China da Afrika
05/09/2024 Duración: 09minAn fara taron shekara-shekara don kyautata hulɗa tsakanin China da Afirka wanda ya samo asali kimanin shekaru 24 da suka gabata. Alƙaluma sun tabbatar da cewa China ita ce ƙasar da nahiyar Afirka ta gudanar da hulɗar tattalin arziki da kasuwanci fiye da kowace nahiya, yayin da a ɗaya bangare bashin da China ke bin Afirka ke ci gaba da ninkawa ninkin-ba-ninkin.Meye ra’ayoyinku a game da kamun lodayin China a fagen tattalin arziki, siyasa da kuma zamantakewa a nahiyar Afirka?Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Alheri Haruna.
-
Yadda batun ci gaba da biyan tallafin mai a Najeriya ya janyo cecekuce
20/08/2024 Duración: 10minShirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan mako ya duba yadda ake fama da matsalar karancin main fetur a Najeriya, wasu bayanai na nuni da cewa yanzu haka gwamnatin ƙasar ta ware naira triliyan 6 da bilyan 800 a matsayin kuɗin tallafi mai a ƙasar.Bayanai sun ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne don biyan tallafin tun daga watan agustan bara har zuwa disambar wannan shekara ta 2024 wato wata watanni 17 cur. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara
-
Ra'ayoyin masu saurare kan gudummawar marigayi Issa Hayatou ga kwallon ƙafa
12/08/2024 Duración: 10minA makon jiya ne Allah ya yiwa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Afirka Issa Hayatou rasuwa, bayan gajeruwar rashin lafiya. Hayatou da ya kwashe kusan shekaru 30 yana jagorancin hukumar, ya taka rawa sosai wajen ci gaban kwallon kafa a nahiyar, musamman bangaren matasa da kuma ganin an kara wa kasashen Afirka gurbi a gasar cin kofin duniya daga gurabe 2 zuwa 5.Shin kun gamsu da gudumawar da ya bayar?Kamar da me za ku tuna wannan gwarzo?