Dandalin Fasahar Fina-finai

Informações:

Sinopsis

Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya  bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.

Episodios

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - ko yaya ake shirya fim a Najeriya ?

  Dandalin Fasahar Fina-finai - ko yaya ake shirya fim a Najeriya ?

  31/01/2021 Duración: 20min

  A cikin shirin fina-finai,Hawa Kabir ta samu zantawa da masu shirya Fim a Najeriya,domin jin ko a ina aka kwana dangane da batun shirya fim a kasar,yanayin rayuwar yan Fim a Najeriya. Hama Kabir ta dubo wasu daga cikin labaran da suka shafi Duniyar yan Fim a Indiya a cikin wannan shirin na Dandalin fasahar fina-finai.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Muhimmancin masanaantar shirya fina-finai wajen samar da ayyukan yi (2)

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Muhimmancin masana'antar shirya fina-finai wajen samar da ayyukan yi (2)

  17/01/2021 Duración: 20min

  Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya cigaba da tattaunawa da  shugaban hukumar tace fim na jihar Kano kan wasu muhimman al'amuran da suka danganci masa'antar .

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Muhimmancin masanaantar shirya fina-finai wajen samar da ayyukan yi

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Muhimmancin masana'antar shirya fina-finai wajen samar da ayyukan yi

  10/01/2021 Duración: 20min

  Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna da shugaban hukumar tace fim na jihar Kano kan wasu muhimman al'amuran da suka danganci masa'antar shirya fina-finai.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Tasirin shirya fina-finai a Najeriya

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Tasirin shirya fina-finai a Najeriya

  03/01/2021 Duración: 20min

  A cikin shirin Dandalin fasahar Fina-finai Hawa Kabir ta samu zantawa da masu shirya fim a Najeriya domin jin halin da suke da kuma jin irin kalubalen da suke fuskanta a Duniyar Fina-finai da muka sani da Nollywood.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Aishatu Aliyu Kaduna yar wasan fim a Najeriya

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Aishatu Aliyu Kaduna yar wasan fim a Najeriya

  20/12/2020 Duración: 20min

  A cikin shirin Duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da Aishatu Aliyu Kaduna,wacce ta yi bayyani dangane da rayuwarta a fani fina-finai,banda haka ta kuma yi bayyani dangane da irin kalubalen da ta yi fama da su a wannan mataki.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Rayuwar yan wasan fina-finai a Najeriya

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Rayuwar yan wasan fina-finai a Najeriya

  06/12/2020 Duración: 20min

  A cikin shirin Dandalin fasahar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da jarumi Ismail,daya daga cikin masu shirya fina-finai a Najeriya. Sau dayawa ,jarumin a duniyar fina-finai a Najeriya kan yi fice tareda neman ilimi a fanoni da dama kamar dai yada zaku ji a wannan shiri.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Rayuwar yan wasan Fim a Najeriya musaman bangaren Nollywood

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Rayuwar yan wasan Fim a Najeriya musaman bangaren Nollywood

  29/11/2020 Duración: 20min

  A cikin shirin na wannan mako,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da wasu yan Fim a Duniyar Nollywood, wandada suka kuma yi mata bayyana dangane da rayuwar su. Duniya Nollywood na fuskantar  dinbin matsaloli da yan wasan ke fatan hukumomi za su taimaka don kawo karshen su,wanda hakan zai bayar da damar raya sashen fina-finai a Najeriya.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Mai Kwashewa ya yi karin haske a game da fim dinsa mai taken Manyan Mata

  Dandalin Fasahar Fina-finai - 'Mai Kwashewa' ya yi karin haske a game da fim dinsa mai taken "Manyan Mata"

  21/11/2020 Duración: 20min

  A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai' na wannan mako, Hauwa Kabir ta duba batutuwa da dama inda har ta kawo fitaccen mai shirya fina finai Abdul Mai kwashewa, wanda ya yi karin haske a kan sabon fim dinsa mai fitowa, 'Manyan Mata'.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Tasirin tufafi a rayuwar dan Fim

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Tasirin tufafi a rayuwar dan Fim

  15/11/2020 Duración: 20min

  A cikin shirin Duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta mayar da hanakali tareda duba tasirin tufafi a duniyar yan Fim a Najeriya,ta kuma yi amfani da wannan dama don jin ta bakin wasu daga cikin masu shirya fim a Najeriya. Sai ku biyo mu

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Rahma Sadau ta nemi afuwa a game da cece - kucen da hotonta ya haddasa

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Rahma Sadau ta nemi afuwa a game da cece - kucen da hotonta ya haddasa

  08/11/2020 Duración: 19min

  A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai', Hauwa Kabir ta duba mana batun cece- kucen da hoton Rahma Sadau ya haddasa, da kuma afuwa da ta nema a sakamakon batancin da ya janyo wa Musulunci.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Matsaloli dake janyo koma baya a Duniyar Fina-finai

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Matsaloli dake janyo koma baya a Duniyar Fina-finai

  01/11/2020 Duración: 20min

  Hawa Kabir ta jiyo ta bakin masu shirya Fim a Najeriya dangane da wannan matsala da ta shafi yan wasa wanda akasari ke janyo mutuwar tauraro a Duniyar Fim. Dandalin fina-finai na daga cikin hanyoyin da sashen hausa na RFI ke baiwa masu shriya Fim damar nuna ci gaba da ake samu a wannan sashe kama daga gida Najeriya zuwa kasashen ketare.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Masu shirya fina-finai yan arewa na nisanta kan su daga zanga-zanga

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Masu shirya fina-finai yan arewa na nisanta kan su daga zanga-zanga

  25/10/2020 Duración: 20min

  A cikin shirin Duniyar Fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da masu shirya Fina-finai a arewacin Najeriya,biyo bayan zanga-zanga da ta rikide zuwa tarzoma dama hadasa mutuwar mutane a wasu yankunan kasar ta Najeriya. Masu shirya fina-finai a arewacin Najeriya sun nisanta kan su daga masu tada kayar baya.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Fannonin masanaantar fina-finai da jarumai ke bada gudunmawa

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Fannonin masana'antar fina-finai da jarumai ke bada gudunmawa

  18/10/2020 Duración: 20min

  Shirin Dandalin Fasahar Fina-finai na wannan makon ya tattauna da jarumai kan fannonin da suke baiwa gudunmawa a masana'tar fim, baya ga haskawa a wasanni.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Gwamnatin Kaduna ta mallakawa masanaantar Kannywood katafaren fili

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Gwamnatin Kaduna ta mallakawa masana'antar Kannywood katafaren fili

  11/10/2020 Duración: 20min

  Shirin 'Dadalin Fasahar Fina-Finai' a wannan karon ya tattauna da masu ruwa da tsaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, kan nasarar da suka samu ta samun kyautar katafaren fili daga gwamnatin jihar Kaduna.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Tarin Mawaka sun aika taaziyyar sarkin Zazzau Alhaji Dr Shehu Idris ta sakon wake

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Tarin Mawaka sun aika ta'aziyyar sarkin Zazzau Alhaji Dr Shehu Idris ta sakon wake

  06/10/2020 Duración: 20min
 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Duniyar Fina-finai a Najeriya

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Duniyar Fina-finai a Najeriya

  27/09/2020 Duración: 20min

  A cikin shirin Duniyar fina-finai,za ku ji halin da yan fim suka samu kan su bayan mutuwar Sarkin Zazzau kamar yada Hawa Kabir ta samun zantawa da wasu dake ruwa da tsaki a wannan fani. Sai ku biyo mu..

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Umar Yahya Malumfashi Bankaura kan lamurran da suka shafi Kannywood (2)

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Umar Yahya Malumfashi 'Bankaura' kan lamurran da suka shafi Kannywood (2)

  20/09/2020 Duración: 20min

  Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan lokaci ya cigaba da tattaunawa ne tare da Umar Yahya Malumfashi kan dalilan da suka janyo kalubalantar masu sana'ar fina-finai kan tarbiya.  

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Umar Yahya Malumfashi (Bankaura) kan lamurran da suka shafi Kannywood

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Umar Yahya Malumfashi (Bankaura) kan lamurran da suka shafi Kannywood

  17/09/2020 Duración: 20min

  Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna da Umar Yahya Malumfashi da aka fi sani da Bankaura, kan batutuwa daban daban da suka shafi masana'antar Kannywood, ciki har da zargin da ake yiwa wasu daga cikin 'yan masana'antar fina-finan da bata tarbiyar al'umma.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Dalilan da suka haifar da koma baya a kasuwar fina finai

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Dalilan da suka haifar da koma baya a kasuwar fina finai

  02/08/2020 Duración: 20min

  A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai' na wannan mako, Hauwa Kabir ta duba dalilan da suka janyo  koma baya a kasuwar fina finan Hausa, da m sauran batutuwa.

 • Dandalin Fasahar Fina-finai - Yadda masu sanaar fim ke kiyaye dokar bada tazara a lokacin annobar coronavirus

  Dandalin Fasahar Fina-finai - Yadda masu sana'ar fim ke kiyaye dokar bada tazara a lokacin annobar coronavirus

  26/07/2020 Duración: 20min

  Shirin 'Dandslin Fasahar Fina Finai' tare da Hauwa Kabir ya yi dubi daa yadda masu sana'ar fim a masana'antar Kannywood a Najeriya ke kiyaye dokar tazara a yayin daukar fim a lokacin annobar coronavirus.

página 1 de 2